Sarkin Musulmi a Najeriya Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci Musulmai akan su saka ido domin neman watan Shawwal 1441 bayan hijira daga ranar Juma’a, 22 ga watan Mayu.

Sanarwar ta fito ne ta hannun shugaban Kwamitin bada shawarwari akan harkokin addini na masarautar Sokoto Farfesa Sambo Junaidu.

“Ana baiwa Musulmai umarnin neman sabon wata, kuma idan aka ganshi a sanar wa dagacin unguwa ko hakimin da yafi kusa, da haka har bayanin ya kai ga Sarkin Musulmi.”

A halin da ake ciki kuma, Sarkin Musulmi ya bada umarni ga masu unguwa da shuwagabannin kauyuka da limamai na Masallatan Juma’a akan su jagoranci Sallolin Idi a Masallatan su, sannan kar a bude Masallatan Idi.

Wannan mataki ya zo ne domin yunkurin dakile yaduwar cutar Korona dake kalubalantar duniya baki daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *