Yunusa Dahiru da a ka fi sani da Yunusa Yellow

Wata babbar Kotun Tarayya a garin Yenagoa da ke jihar Bayelsa ta yanke wa matashin nan dan jihar Kano Yunusa Dahiru (Yellow) hukuncin dauri shekaru ashirin da shida a gidan wakafi sakamakon samunsa da laifin fasa kwaurin wata budurwa Ese Rita Oruru ‘yar shekaru goma sha uku da haihuwa zuwa Kano tare da aikata lalata da ita ta haramtacciyar hanya bayan ya Musuluntar da ita, tare da canza mata suna zuwa Aisha da kuma yi mata ciki. 

Ese Rita Oruru

Idan ba a manta ba, a shekarar 2015 ne labarin wani matashi dan jihar Kano ya cika gari game da zargin ya sace wata kwailar yarinya Ese da cewa ya gudu da ita zuwa Kano bayan ya aureta ba bisa yardar iyayenta Charles da Rose ba ‘yan al’ummar Uwheru da ke garin Ughelli a jihar Delta ta Najeriya.

Inda daga baya ‘yan sanda suka cafke shi tare da tseratar da yarinyar zuwa ga iyayenta a lokacin tana dauke da cikinsa na watanni biyar. Tun lokacin a ke ta jani in jaka a lamarin da yake neman rikidewa zuwa maganar kabilanci da ta addini. Alkalin kotun Jane Inyang ta wanke matashin daga zargin laifin farko na cewa garkuwa ya yi da yarinyar. 

To amma Alkali ta daure shi bisa laifi na biyu har tsawon shekaru biyar bisa laifin fataucin yarinyar, sai kuma daurin shekaru bakwai a kan laifi na biyu na laifin aikata lalata da ita ta haramtacciyar hanya. Haka kuma ya sake samun daurin shekaru bakwai na aikata amfani da damar saduwar jima’i don biyan bukatar kansa. 

Sai kuma wani daurin shekaru bakwan bisa laifin ‘saduwar jima’in banza ta fadi ba bisa ka’ida ba. A jimlance zai kwashe shekaru ashirin da shida a gidan yari, matukar ba wata kotun da ke gaban wannan da ta yi hukuncin nan ce ta yanke wani hukuncin ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *