Daya daga cikin mutanen da aka fi nema dangane da kisan kare dangin Ruwanda na 1994, Felicien Kabuga ya bayyana a gaban wani kotun Faransa Larabannan, kwanaki kalilan bayan tsare da shi da aka yi, amma an dakatar da yanke masa shawara sai mako mai zuwa.

Kabuga mai shekaru 84 a duniya, an tsare shi ne a kusa da birnin Paris ranar Asabar bayan share shekaru 25 da tserewa. An shigar da shi zauren kotun bayan akan keken kujera yana sanye da takunkumi a bakinsa. Ya dade yana zama a arewacin birnin Paris, inda ‘ya’yan shi suka boye shi, sannan yana amfani da sunan bogi.

Kabuga wanda aka saka kyautar dalar Amurka miliyan biyar ga duk wanda ya samo shi, ana zargin shi ne da baiwa mayakan sa kai makamai a kisan kare dangin da yayi ajalin rayukan ‘yan kabilar Tutsi su wajen dubu dari takwas da ‘yan Hutu da suka yi kokarin kare su.

Yanzu haka dai kotun ta dakatar da yanke masa hukunci ne, saboda tana kokarin yanke shawara akan ko ta mika Kabuga ga wata kotun Kasa da Kasa ta Majalisar Dinkin Duniya a birnin Hague wadda da aka kafa musamman domin kisan kare dangin Ruwanda.

Lauyan Kabuga yace tsohon yana so a yi masa shari’a a Faransa saboda lafiyar sa, amma bai bada karin bayani ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *