Kwanaki kalilan kafin bikin Karamar Sallah, kotun tafi da gidanka ta Jihar Kano dake aiki tare da jami’an tsaro sun tsare motoci arba’in da biyar da suka karya dokar dakatar da tafiye-tafiye tsakanin jihohi.

Motoci misalin 30 an tsare su ne a Kwanar Dangora, bakin iyaka tsakanin Kano da Kaduna.

Wata sanarwar da Sakataren yada labaran gwamnatin Jihar Abba Anwar ya fitar kuma ya sakawa hannu, ta bayyana cewa an riga an ci tarar wadanda suka karyar dokar a gaban kotu domin hukunta su akan laifin da suka yi.

A lokacin da yake yabawa jami’an tsaro akan aikin da suka yi, Gwamnan Jihar Abdullahi Ganduje yayi kira ga ma’aikata akan su cigaba da zuba idanu suna lura domin tabbatarwa bakin iyakokin Kano suna rufe ba tare da mutane sun ketara ba bisa ka’ida ba.

Idan ba’a manta ba, a kwanakin bayannan ne aka ji Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i yana ikirarin cewa zai tsaya da kanshi wajen hana mutane da Kano shiga jihar, lamarin da jawo cacar baki tsakanin mutanen Kano da Kaduna akan shafukan sadarwa.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *