Wani jirgi a sararin samaniya. Hoto: Usman Kabara

A kalla an zakulo wani babban jami’in banki da kuma wani bawan Allah da ransu bayan wani jirgi mai samfurin lamba A320 ya yi hatsari inda ya fada wata unguwa a yankin Karachi da ke kasar Pakistan bayan kagewar injinansa guda biyu, ya kuma hallaka fasinjojin cikinsa sama da dari.

Tuni a ka aike da jami’an kar ta kwana don tantance majinyata da kuma gano wadanda rai yayi halinsa. Sannan Mai Garin Karachi ya tabbatar da mutuwar fasinjoji guda casa’in da kuma ma’aikatan jirgin guda takwas.

Shedun gani da ido sun ga lokacin da jirgin ya ke ta kokarin sauka har kusan sau uku kafin kifewarsa a yunkurin sauka a karo na hudu, bayan direban jirgin ya fadawa masu kula da sauka da tashin jiragen sama a filin jirgi cewa, shi fa ba sauran sa rai da tsira don ya rasa injin jirgin guda daya.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *