Kwamitin da Shugaban Kasa a Najeriya ya nada domin kalubalantar COVID-19 ya bayyana cewa yana shirye-shirye aiwatar da matakai na gaba a yaki da cutar Korona a dai-dai lokacin da zata cigaba da aiki da gwamnonin jihohi.

Ta jaddada cewa gwamnonin jihohi sune ya kamata su dauki linzamin yaki da cutar.

Shugaban masu gudanarwar kasa a kwamitin, Sani Aliyu, ya bayyana hakan ne a sanarwar da ya fitar a birnin Abuja Alhamis dinnan.

Aliyu ya bayyana cewa Kwamitin zai cigaba da tallafa wa gwamnonin jihohi wajen yanke shawarwari da basu bayanan da suke buata, amma baza su cigaba da kawo dauki daga gwamnatin tarayya ba.

Aliyu yace “muna tsammanin gwamnonin jihohi suna da halin aiwatar da matakan da suka dace domin kiyaye rayukan mutanen su.”

“Saboda haka, mu dai ta bangaren mu, gwamnonin Jihohi sune zasu cigaba da daukar nauyin wannan yaki nan gaba.

“Amma muna fata zamu cigaba da aiki da su kut-da-kut domin tabbatar mun yi amfani da kimiyya da kuma la’akari da al-adu da addini wajen ayyana dokoki da sharruda.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *