Ma’aikatan gwamnati a Jihar Kano sun yi kuka da babban murya akan abunda suka kira zaftare albashin su na Mayu ba tare da an sanar da sub a.

Ma’aikatan sun gano cewa an zabtare musu albashin su a lokacin da sakon shigar kudi asusun banki ya riski wayoyin su.

Daya daga cikin ma’aikatan wanda ya so a sakaye sunan sa, ya bayyana cewa ma’aikata dake da matsayinsa sun rasa daga Nera dubu goma da dari uku zuwa dubu goma sha biyu da dari biyu.

Wani ma’aikacin karamar hukuma shima ya bayyana cewa an zabtare albashin sa na watan Mayu da wajen dubu bakwai da dari shida, inda ya kara da cewa akwai ma’aikata da yawa da wannan lamari ya tayar wa hankali.

Ya cigaba da cewa baya tsammanin za’a yanke masa albashi saboda gwamnatin Jihar ta tabbatar wa duka ma’aikata cewa zata zabtare albashin ‘yan siyasa ne kawai, ba na ma’aikatan gwamnati ba.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *