Birnin Cape Town ya zama cibiyar annobar cutar Korona a Afirka ta Kudu, kuma daya daga cikin wuraren da COVID-19 ya fi shafa a duk fadin nahiyar Afirka.

Birnin wanda ya shahara a matsayin wajen bude ido ya samu sama da mutane dubu goma sha biyu da suka kamu da cutar ya zuwa alhamis dinnan, wanda ya kasance kaso sittin da uku cikin dari na mutane dubu goma sha tara da aka samu da cutar a duk fadin Afirka ta Kudu, kuma kaso goma kennan cikin dari na adadin mutane dubu tasa’in da biyar da aka samu a duk fadin nahiyar Afirca.

Masu bincike na kiyasin cewa mutane tsakanin dubu arba’in zuwa dubu arba’in da biyar ne zasu rasa rayukansu a Afirka ta Kudu, kuma mutum miliyan goma shi uku cikin hamsin da bakwai ne ake tunanin zasu kamu da cutar a Afirka ta Kudu.

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *