Wata ‘yar shekaru goma sha takwas mai suna Salma Hassan, wadda ake zargi da caka wa mijin ta wuka har ya mutu a Bauchi tace ta kashe mijinta ne a kokarin ta na kare kanta a lokacin da ya nemi saduwa da ita, kwanaki goma sha daya bayan daura musu aure.

Ta bayyana cewa ta caka mishi wuka ne saboda yaka kokarin yi mata fyade, kuma ta kara da cewa bata san cewa jima’i na daga cikin farillan aure ba.

Salma ta bayyana hakan ne Alhamis dinnan lokacin da ‘yan Sanda suka bayyana ta tare da wasu masu laifuka su ashirin da daya, a cikin su harda ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Bauchi, Philip Maku, a lokacin da yake nunawa manema labarai mutanen da ake tuhuma da laifuka a shedkwatar Jihar, ya bayyana cewa an kama Salma ne rike da wutar da ake zargin ta aikata laifin da shi, a gidanta dake karamar hukumar Itas-Gadau.

“An caka wa marigayi Mohammed Mustapha wuka ne a kirji”.

“Sakamakon haka ne ya samu rauni mai tsanani kuma aka garzaya da shi babban asibitin Itas-Gadau domin duba shi inda ya cika.

“An kama wadda ake zargi da aikata laifin, kuma ta amince akan cewa ta aikata wannan laifi.

“Shaidar da aka samu daga wajen wadda ake zargi da laifin wuka ce,” a cewar Kwamishinan.

A ‘yar karamar tattaunawa da tayi da manema labarai, Salma Hassan ta bayyana cewa mijin nata yana nema ne yayi mata fyade, tana jaddada cewa ita bata san cewa saduwa na daga cikin farillan aure ba.

“A rana ta goma sha daya da auren mu, ya kusance ni domin saduwa, ni kuma na ki amincewa saboda ban taba yi a baya ba.

“Na dauka fyade yake kokarin yi mun, amma sai ya fusata, yana kokarin yin amfani da karfi domin kusanta ta har yana duka na.

“Shine na dauki wuka domin na razana shi ya kyale ni, amma sai ya cigaba da zuwa, har ta kaiga ban san lokacin da na caka mishi wukar a kirji ba.

“Ban yi niyyar kashe shi ba, kuma nayi nadamar abunda nayi,” ta kara da cewa.

Shugaban ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa rundunar shi ta kama gungun mutum hudu masu garkuwa da mutane dangane da sacewa da kashe wani yaro dan shekaru goma sha biyar biyo bayan karbar kudin fansa har na Nera miliyan biyar da dubu dari biyar daga iyayen shi.  

Rubuta ra’ayi

Your email address will not be published. Required fields are marked *